logo

HAUSA

Sin ta bukaci a yi watsi da tunani irin na cacar baka game da batun Ukraine

2022-02-25 19:48:15 CRI

Sin ta bukaci a yi watsi da tunani irin na cacar baka game da batun Ukraine_fororder_1c01-e0428e7b1fe47141ca255fb100c41a73

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya ce Sin na fatan dukkanin sassa masu ruwa da tsaki za su yi watsi da tunani irin na cacar baka, game da takaddamar Ukraine, kuma su kafa wani tsarin kiyaye tsaron nahiyar Turai mai daidaito da kuma inganci, ta hanyar komawa tattaunawa da gudanar da shawarwari.

Wang Wenbin, wanda ya bayyana hakan a Juma’ar nan, ya ce Sin na fatan ganin dukkanin sassa, sun rungumi matakan martaba damuwar junan su ta fuskar tsaro, tare da kaucewa abubuwan da za su iya rura wutar yaki. (Saminu)