logo

HAUSA

Ofishin hukumar Siyasa na kwamitin kolin JKS ya yi zama domin tattaunawa game da rahoton daftarin ayyukan gwamnati

2022-02-25 21:14:04 CRI

Hukumar Siyasa ta kwamitin kolin JKS ya yi zama a yau Juma’a, domin tattaunawa game da daftarin rahoton ayyukan gwamnati, wanda majalisar gudanarwar kasar za ta mika ga majalissar wakilan jama’ar kasar, yayin taron ta na shekara shekara dake tafe. 

Yayin taron, wanda babban sakataren kwamitin kolin JKS Xi Jinping ya jagoranta, an kuma duba kan rahotanni guda biyu, na sashen sanya ido da ladaftarwar JKS.  (Saminu)