logo

HAUSA

ECOWAS za ta gaggauta samar da kiwon lafiya na bai daya zuwa shekarar 2030

2022-02-25 14:04:38 CRI

ECOWAS za ta gaggauta samar da kiwon lafiya na bai daya zuwa shekarar 2030_fororder_0225-Faeza-ECOWAS

Kungiyar raya tattalin arzikin yammacin Afrika (ECOWAS), karkashin hukumarta ta lafiya WAHO, na da burin gaggauta samar da kiwon lafiya na bai daya ga dukkan kasashe mambobinta zuwa shekarar 2030.

Darakta janar na hukumar lafiyar ta WAHO Stanley Okolo ne ya bayyana hakan yayin bude wani taron manyan jami’ai game da jagorantar ayyukan lafiya na bai daya da babban taron majalisar ministocin lafiya na kasashen kungiyar.

Stanley Okolo ya bayyana cewa, burin hukumar zuwa shekarar 2030, wanda ya yi daidai da muradun ci gaba masu dorewa na MDD, shi ne cimma burin hukumar a wani yanayi da tsarin kiwon lafiya ke sauyawa cikin sauri.

Ya bukaci daftari na karshe da zai fito ya kasance wanda zai shawo kan bukatun lafiya na yankin da cimma burin tafiya tare da kowa. (Fa’iza Mustapha)