logo

HAUSA

Xi Jinping ya zanta da takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin ta wayar tarho

2022-02-25 20:50:07 cri

Xi Jinping ya zanta da takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin ta wayar tarho_fororder_4dcb6fd25fca4d6ebf0c01a2e93f61d0

A yau Juma’a ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya zanta da takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin ta wayar tarho. Yayin zantawar, Xi Jinping ya sake godewa Putin, bisa zuwan sa kasar Sin don halartar bikin bude gasar wasannin Olympics na lokacin sanyi ta birnin Beijing, ya kuma taya 'yan wasan kasar Rasha murnar samun matsayi na biyu a jerin lambobin yabo.

A nasa bangaren, Putin ya taya daukacin jama'ar kasar Sin murna, bisa cikakkiyar nasarar da aka samu wajen shirya gasar Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing, da kuma yadda tawagar kasar Sin ta nuna bajinta. Baya ga haka, bangarorin biyu suka yi musayar ra’ayoyi kan halin da ake ciki a kasar Ukraine.

Putin ya gabatar da asalin tarihin batun Ukraine, da kuma halin da ake ciki na aiwatar da matakan soji da kasarsa ke yi a gabashin Ukraine, da matsayin da kasarsa ta dauka. Ya kara bayyana cewa, Amurka da NATO, sun dade suna watsi da damuwar Rasha kan tsaron kasa yadda ya kamata, tare da yin watsi da alkawurran da suka dauka, kuma suna ci gaba da tura sojoji zuwa gabas, suna kuma kalubalantar hakurin Rasha. A cewarsa, Rasha a shirye take ta gudanar da shawarwari bisa babban matsayi da Ukraine.

Game da hakan, Xi Jinping ya nuna cewa, kasar Sin ta yanke shawara kan matsayinta ne bisa la'akari da cancantar batun Ukraine. Ya ce ya kamata a yi watsi da tunanin yakin cacar baka, da ba da muhimmanci, da mutunta halastacciyar kulawar dukkan kasashe a fannin tsaro, da samar da tsarin tsaron Turai mai daidaito, inganci da dorewa, ta hanyar yin shawarwari. Kana kasar Sin tana goyon bayan Rasha, da ta yi shawarwari da Ukraine don warware matsalar. Kaza lika ko da yaushe kasar Sin na daukar matsayin mutunta mulkin kan kasa, da cikakken yankin kasa na kasashe daban daban, da kiyaye manufofi, da ka'idojin kundin tsarin mulkin MDD.  (Mai fassara: Bilkisu Xin)