logo

HAUSA

Putin ya tattauna batun Ukraine da shugabannin kasashen duniya

2022-02-25 10:02:37 CRI

Putin ya tattauna batun Ukraine da shugabannin kasashen duniya_fororder_0225-Faeza-Putin

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya tattauna jiya Alhamis da shugabannin kasashen duniya da dama ta wayar tarho.

Putin ya tattauna ta wayar tarho da shugaban Iran Ebrahim Raisi, inda ya yi masa bayani game da yadda yanayin batun Ukraine ke wakana.

A nasa bangare, shugaba Raisi ya ce ya fahimci damuwar Rasha dangane da tsaro, wadanda matakan Amurka da kungiyar NATO suka haifar.

Har ila yau, Putin ya yi wa Firaministan India Narendra Modi, bayani game da matsayar kasar kan batun Ukraine.

Putin da takwaransa na Faransa, Emmanuel Macrom ma, sun tattauna ta wayar tarho kan yanayin na Ukraine.

A jiya Alhamis ne shugaba Vladimir Putin ya bada umarnin wani matakin soji na musamman a yankin Donbass, inda Ukraine ta tabbatar da cewa an kai wa sansanoninta na soji hari. (Fa’iza Mustapha)