logo

HAUSA

An kyale Ukraine ita kadai ta yaki Rasha

2022-02-25 10:27:48 CRI

An kyale Ukraine ita kadai ta yaki Rasha_fororder_0225-Ukraine-Faeza

Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelenskyy, ya bayyana a yau Juma’a cewa, an kyale kasarsa ita kadai ta yaki Rasha, bayan da Fadar Kremlin ta sanar da daukar matakan soji na musamman a yankin Donbas.

Ya kuma kara da cewa, ba ya tsoron hawan teburin sulhu da Rasha kan batutuwan da suka hada da matsayin Ukraine da tabbacin tsaro. (Fa’iza Mustapha)