logo

HAUSA

A shekarar 2021, jarin da Sin ta zuba a fannin binciken kimiyya zai iya kaiwa kusan yuan triliyan 2.79

2022-02-25 13:57:22 CRI

A shekarar 2021, jarin da Sin ta zuba a fannin binciken kimiyya zai iya kaiwa kusan yuan triliyan 2.79_fororder_0225-Ahmad-kimiya

Ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya gudanar da taron ’yan jaridu a yau, inda ya gabatar da ci gaban da aka samu a fannonin kimiyya da fasahar kirkire kirkire na kasar.

Game da jimillar ci gaban da fannin ayyukan kimiyya da fasaha na kasar Sin ya samu a shekarar 2021, an gabatar a wajen taron cewa, jimillar jarin da aka zuba a fannin bincike da bunkasa ci gaban kimiyya da fasaha, ya kai RMB Yuan triliyan 2.79, wato an samu karin kashi 14.2 bisa 100, sama da na shekarar 2020, kuma jimillar alkaluman jarin da aka zuba a fannin bincike da raya cigaba, wato R&D, idan an kwatanta da matsayin GDPn kasar, ya kai kashi 2.44 bisa 100, sannan gundarin kudaden da aka zuba ya karu da kashi 15.6 bisa 100 idan an kwatanta da na shekarar 2020, yayin da jimillar adadin jarin na R&D ya kai kashi 6.09 bisa100, kuma cikakken girman matsayin kirkire-kirkire na kasar Sin ya karu zuwa matsayi na 12 a duniya. (Ahmad Fagam)