logo

HAUSA

Biden ya sanar da kakabawa Rasha karin takunkumai

2022-02-25 09:48:55 CRI

Biden ya sanar da kakabawa Rasha karin takunkumai_fororder_0225-Faeza-Biden

Shugaban Amurka Joe Biden ya sanar da kakaba karin takunkumai kan Rasha, tare da tura karin dakaru zuwa Turai, yayin da ake ci gaba da rikici kan Ukraine.

Da yake jawabi daga fadar White House, shugaba Biden ya ce sabbin matakan za su mayar da hankali kan manyan bankunan Rasha da takaita karfin kasar na cinikayya cikin takardun kudaden Dala da Euro da Fam da Yen, da kuma rage fitar da kayayyakin fasaha na kasar da karfinta na daga karfin rundunarta na soji.

Shugaban na Amurka ya ce ya bada umarnin tura sojojin sama da na kasa dake Turai zuwa yankin gabas, tare da tura wasu zuwa Jamus, a matsayin wani bangare na matakan martani na NATO. (Fa’iza Mustapha)