logo

HAUSA

WHO:Za a ingiza aikin yiwa al’ummar Afrika allurar rigakafin cutar COVID-19

2022-02-25 10:21:26 CRI

Sashin Afrika na WHO ya yi taron manema labarai a birnin Brazzaville hedkwatar jamhuriyyar Kongo jiya Alhamis, inda aka gabatar da cewa, shekara daya bayan samarwa nahiyar Afrika allurar rigakafin cutar COVID-19 karkashin shirin “COVAX”, yawan allurar da aka yiwa al’ummar nahiyar ya kai miliyan 400. Wannan shi ne aiki mafi girma da aka yiwa al’ummar Afrika kan annoba, amma ana bukatar yiwa karin al’umma allurar.

Ya zuwa yanzu, mutanen da yawansu ya kai kashi 13% kacal aka yiwa allurar, daga ciki, allurar da aka yi wa al’ummar kasashe 18 ba ta kai kashi 10% ba, haka kuma, yawan alluarar da aka yiwa kasashe 3 daga cikinsu bai kai 1% ba. Ban da wannan kuma, yawan allurar da kasashe 29 suka yi amfani da su bai wuce kashi 50% ba, abin da ya sa yawan mutanen da aka yiwa allurar a nahiyar ya yi kasa da na sauran nahiyoyi matuka.

WHO za ta yiwa al’ummar duniya allura a mataki-mataki a wurare daban-daban. Ya zuwa yanzu, an tabbatar da baiwa kasashe 20 mafi bukatar taimako, inda aka samar da allura a cibiyoyin sayar da kayayyaki da kasuwanni da kauyuka masu nisa na kasashe 10 tare da samun nasara. (Amina Xu)