logo

HAUSA

Sin na da masaniya game da damuwar Rasha ta fuskar tsaro

2022-02-24 20:59:58 CRI

Sin na da masaniya game da damuwar Rasha ta fuskar tsaro_fororder_3ac79f3df8dcd1009d4ac31c155c6018b8122f13

Babban dan majalissar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya ce batun kasar Ukraine na da sarkakiya, da kuma tushe na tarihi, kuma Sin na da masaniya game da damuwar Rasha ta fuskar tsaron kasa.

Wang Yi, wanda ya bayyana hakan a Alhamis din nan, yayin zantawarsa ta wayar tarho da takwaransa na Rasha Sergei Lavrov, ya sake jaddada matsayar Sin, ta martaba ikon mulkin kai, da daukacin yankuna na dukkanin kasashe.

A nasa bangare, Mr. Lavrov ya yi bitar takaddamar kasar sa da Ukraine, tare da fayyace matsayin Rasha. Ya ce Amurka da kungiyar tsaro ta NATO, ba su cika alkawarin da suka dauka ba, inda suka ci gaba da fadada ikon su a yammacin iyakar Rasha, sun kuma ki aiwatar da sabuwar yarjejeniyar Minsk, tare da keta yarjejeniyar da aka cimma karkashin kudurin dokar kwamitin tsaron MDD mai lamba 2202 na shekarar 2015.

Daga nan sai Mr. Lavrov ya sake jaddada cewa, matsin da Rasha ta fuskanta ne ya tirsasa ta daukar matakan wajibi, na kare hakkoki da moriyar ta. (Saminu)