logo

HAUSA

Rasha ta rufe sararin samaniyar kan iyakokinta da Ukraine da Belarus

2022-02-24 13:58:05 CRI

Rasha ta rufe sararin samaniyar kan iyakokinta da Ukraine da Belarus_fororder_220224-Fa'iza-Ukraine

Hukumar kula da sufurin jiragen sama ta Rasha, ta sanar a yau Alhamis cewa, kasar ta rufe zirga-zirgar jiragen fasinja a sararin samaniyarta dake yankin yammacin kasar, wanda kuma ke iyakokinta da Ukraine da Belarus. Hukumar ta sanar da hakan ne jim kadan bayan shugaba Vladimir Putin, ya bada umarnin wani aikin soji na musamman a yankin Donbass.

An kuma ji karar ababen fashewa a Kiev, babban birnin Ukraine da safiyar yau Alhamis. (Fa’iza Mustapha)