logo

HAUSA

Dangantakar dake tsakanin Sin da Rasha ta sha bamban da dangantakar dake tsakanin Amurka da sauran wasu kawayenta

2022-02-24 21:21:34 cri

Dangantakar dake tsakanin Sin da Rasha ta sha bamban da dangantakar dake tsakanin Amurka da sauran wasu kawayenta_fororder_b372687f0c2f433692b247bf480bbdb9

A yayin da take mayar da martani ga kalaman mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Amurka Ned Price, dake alakanta da kasar Sin da batun Ukraine, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying, ta bayyana a yau Alhamis cewa, dangantakar dake tsakanin Sin da Rasha, ta dogara ne kan ra’ayin ba ruwanmu, ba nuna adawa, kana ba za ta goyi bayan hari kan bangare na uku ba, wanda hakan ya sha bamban da yadda Amurka ke yi, ta hanyar kafa “kananan kungiyoyi” bisa bambancin ra’ayi, da rura wutar adawa da rarrabuwar kai.

Hua ta kara bayyana cewa, game da batun yadda za a mutunta mulkin kan kasa, da kuma cikakken yankin kasa, Amurka ba ta cancanci ta gaya wa kasar Sin abin da ya kamata ta yi ba. Ta ce jama'ar kasar Sin suna da ainihin fahimta kan mulkin kan kasa, da kuma cikakken yankin kasa.

Baya ga haka, Hua ta nuna cewa, a cikin kasa da shekaru 250 da kafuwar kasar Amurka, shekarun da ta shafe ba ta gudanar da ayyukan soji a kasashen waje ba sun kai 20. Har kullum ta kan fake da dalilai na kare dimokuradiyya, ko hakkin dan adam wajen kaddamar da yaki, har ma a wasu lokutan dalilan nata ba sa wuce karamar kwalbar hoda, ko kuma labarin karya.

Game da maganar Amurka a fakaice, cewa wai kasar Rasha ta dauki mataki ne saboda goyon baya da ta samu daga kasar Sin, Hua ta bayyana cewa, Rasha mamba ce ta dindindin a kwamitin sulhu na MDD, kuma kasa ce mai cin gashin kanta, kuma bangaren Rasha yana tsarawa, da aiwatar da dabarun diflomasiyya bisa ga matsayar kasar da muradun ta. (Bilkisu Xin)