logo

HAUSA

Kakaba takunkumi ba zai dakile yakin da ya barke ba

2022-02-24 19:03:06 CRI

Kakaba takunkumi ba zai dakile yakin da ya barke ba_fororder_50e8936022454fed90edcd4e7f67380b

Yayin da wasu rahotanni ke cewa, wasu ayarin motocin sojin kasar Rasha sun fara tsallakawa kudancin kasar Ukraine, kuma sojojin Rashan sun harba makaman atilari cikin yankunan na kudanci, sassan kasa da kasa sun bayyana rashin jin dadi da yadda takaddamar da aka jima ana kokarin yayyafawa ruwa ta rikide zuwa yaki.

Tsagin Ukraine dai na cewa, ayarin sojojin Rasha sun ratsa ƙasarta ta sashen arewa daga Belarus, da kuma ta gabas daga Rashar. Ko shakka ba bu wannan batu zai kasance a sahun gaba, cikin muhimman batutuwa mafiya jan hankalin masharhanta, duba da yadda rikicin siyasar kasar Ukraine din ya sauya salo, kuma damar sasantawa cikin ruwan sanyi ke neman “gagarar kundila”.

A bangaren Ukraine, mahukuntan kasar na ci gaba da shan alwashin kare rayukan fararen hula, har ma sun yi ikirarin harbo wasu jiragen Rasha biyar, da kuma jirgi ɗaya mai saukar ungulu na ƙasar.

Yayin da hakan ke wakana, tuni wasu sassan kasashen turai, da na yammacin duniya, suka fara tofa Albarkacin bakin su, inda shugabar hukumar tarayyar Turai, Ursula von der Leyen, da shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz, da Firaiministan Birtaniya Boris Johnson, da Firaiministan Italia Mario Draghi, suka soki Rasha da cewa ta dauki mataki maras dacewa. A hannu guda, sun jaddada goyon baya ga matakin da Amurka ta ayyana tun da fari, na kakabawa Rasha takunkumai masu ƙarfi nan ba da jimawa, a wani mataki na raunata tattalin arziƙin ta da kuma ci gabanta. To sai dai abun tambayar shi ne, shin wannan mataki zai haifar da da mai ido?

Tarihi ya jima da tabbatar da cewa, sanyawa kasashe takunkumi bai taba warware yanayi mai tsanani musamman irin na yaki ba. Kuma idan aka yi la’akari da karfin Rasha a fannin samar da makamashi da kere kere, wannan mataki ba abun da zai haifar illa jefa tsarin tattalin arzikin duniya cikin mawuyacin hali. Tuni ma dai farashin danyen mai a kasuwannin duniya ya fara dagawa, wanda hakan zai shafi matakin farfadowar tattalin arzikin kasashe da dama.

Don haka masharhanta da dama ke ganin maimakon daukar matakin sanya takunkumi ga Rasha, kamata ya yi sassan kasa da kasa su goyi bayan sulhunta rikicin ta hanyar komawa teburin sulhu da shiga tsakani. Kaza lika kasashen yamma musamman Amurka, su kauracewa tura makamai ko dakarun soji da nufin shiga yaki a Ukraine, domin kuwa hakan ba abun da zai haifar illa kara rura wutar yaki, da gurgunta zamantakewar fararen hula.

Cikin shekaru sama da 20 da suka gabata, Amurka na kara kakabawa kasashe daban daban takunkumai, inda yayin jagorancin tsohon shugaban kasar Donald Trump, kasar ta kakabawa kasashe daban daban takunkumai sama da 3,800. Kaza lika daga shekarar 2011 kawo yanzu, Amurka ta kakabawa Rasha takunkumai sama da 100. Amma me wadancan takunkumai suka haifar kawo yanzu?

Idan har ba su haifar da wani sakamako mai gamsarwa ba, ta yaya sabbin takunkuman na yanzu za su kai ga warware yakin da ya barke? Don haka dai ba abun da ya ragewa sassan kasa da kasa a yanzu, wanda ya wuce shiga tsakani, da komawa tattaunawa da dukkanin fannonin da wannan lamari ya shafa. (Saminu Alhassan)