logo

HAUSA

Majalisar dokokin Rasha ta amince da bukatar amfani da sojoji a ketare

2022-02-23 10:24:46 CRI

Majalisar dokokin Rasha ta amince da bukatar amfani da sojoji a ketare_fororder_220223-A2-Rasha

Majalisar tarayyyar Rasha ko kuma babban majalisar dokoki ta kasa, a ranar Talata ta amince da bukatar da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin, ya gabatar mata, na neman amfani da sojoji a kasashen ketare.

Tun da farko a wannan rana, majalisar wakilan Rasha, wato Russia State Duma, a lokacin zamanta, ta amince da yarjejeniyar zumunci, da hadin gwiwar tallafawa juna tsakanin Rashar da kasashen Lugansk (LPR), da Donetsk (DPR). A ranar Litinin, shugaban Rasha ya sanya hannu inda ya amincewa da dokar ’yancin kan LPR da DPR a matsayin kasashe masu cin gashin kansu.

Shugaban kasar Ukrain, Volodymyr Zelensky, ya bayyana a ranar Talata cewa, Kiev ta bukaci kasashen duniya su gaggauta gudanar da taron tattaunawa game da batun matsayar da Rasha ta dauka na amincewa da kafa kasashen Donetsk da Lugansk da suka balle daga shiyyar gabashin Ukraine. (Ahmad)