logo

HAUSA

Ma’aikatar lafiya: Sojojin Isra’ila sun kashe yaron Falasdinawa a yammacin kogin Jordan

2022-02-23 14:23:44 CRI

Ma’aikatar lafiya: Sojojin Isra’ila sun kashe yaron Falasdinawa a yammacin kogin Jordan_fororder_220223-A5-Palasdinu

Sojojin Isra’ila sun kashe wani yaro Bafalasdine dan shekaru 14 da haihuwa a ranar Talata a tsakiyar birnin Bethlehem, dake yamma da kogin Jordan, a cewar ma’aikatar lafiyar kasar Falastinu.

Kamar yadda ma’aikatar lafiyar ta bayyana, Mohammad Shehada, dan shekaru 14 a duniya, ya gamu da ajalinsa ne, bayan da sojojin Isra’ila suka harbe shi, a yayin musayar wuta a garin al-Khader dake kusa da birnin Bethlehem.

Haka zalika, shaidun gani da ido sun ce, an kashe yaron ne a lokacin da rikici ya barke a wannan gari tsakanin sojojin Isra’ila da gwamman Falastinawa da suka fito zanga-zanga.

Sai dai har yanzu babu wani martani daga bangaren sojojin Isra’ilan.

Firaministan Falastinawa, Mohammed Ishtaye, ya fadawa taron ’yan jaridu cewa, gwamnatin Falastinu ta yi Allah wadai da kisan Shehada. Ya kara da cewa, kashe karamin yaro mummunan laifi ne da ya saba dokokin kasa da kasa. (Ahmad)