logo

HAUSA

Wang Yi ya zanta da jami’an IGN game da batun yiwa kwamitin tsaron MDD gyaran fuska

2022-02-23 20:58:55 CRI

Wang Yi ya zanta da jami’an IGN game da batun yiwa kwamitin tsaron MDD gyaran fuska_fororder_8435e5dde71190ef4a64f343c20d731ffcfa60aa

Babban dan majalissar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya zanta da jagororin tsarin shiga tsakani na gwamnatocin kasa da kasa kan batun yi wa kwamitin tsaron MDD gyaran fuska, ko IGN a takaice, wato Alya Ahmed Saif Al-Thani, da Martin Bille Hermann. Jami’an sun zanta ne a jiya Talata ta kafar bidiyo.

Da yake tsokaci yayin tattaunawar, Wang ya ce yayin da ake gudanar da sauye sauye ga kwamitin na tsaron MDD, ya dace a maida hankali matuka ga fadada wakilci, da muryoyin kasashe masu tasowa, ta yadda karin kasashe, musamman kanana da matsakaita za su samu karin damammaki, na shiga a dama da su yayin yanke shawarwari a kwamitin na tsaro. Wang ya ce hakan shi ne tushe, kuma alkiblar sauye sauyen da ake fatan yiwa kwamitin na tsaro.  (Saminu)