logo

HAUSA

Sama da yara miliyan 12.5 sun harbu da COVID-19 a Amurka

2022-02-23 14:15:43 CRI

Sama da yara miliyan 12.5 sun harbu da COVID-19 a Amurka_fororder_220223-A4-Amurka

Sabon rahoton da kungiyar kula da asibitocin kananan yara ta Amurka wato AAP, ta fitar a jiya Talata ya nuna cewa, sama da kananan yara miliyan 12.5 sun kamu da cutar COVID-19 a kasar Amurka tun daga farkon lokacin barkewar cutar.

A cewar rahoton, ya zuwa ranar 17 ga watan Fabrairu, jimillar yara miliyan 12,515,391 sun kamu da cutar COVID-19 a fadin kasar Amurka, kuma adadin yara ya kai kashi 19 bisa 100 na yawan mutanen da suka kamu da cutar a fadin kasar.

An samu karin yara sama da miliyan 1.9 da suka kamu da cutar COVID-19 a kasar cikin makwanni hudun da suka gabata.

A cewar AAP, wannan shi ne mako na 28 a jere, da ake samun kananan yara a Amurka dake kamuwa da cutar wadanda adadinsu ya kan zarce 100,000. Daga satin farko na watan Satumbar bara, an samu kusan karin yara miliyan 7.5 da suka kamu da cutar a Amurka. (Ahmad)