Sin ta yi kira da a daidaita batun Ukraine ta hanyar diplomasiyya
2022-02-22 15:43:33 CRI
A jiya da dare, zaunannen wakilin kasar Sin a MDD, Zhang Jun ya gabatar da jawabi a yayin halartar taron gaggawa da kwamitin sulhun MDD ya kira na yin nazari kan batun Ukraine, inda ya yi kira ga bangarorin da abin ya shafa da su kai zuciya nesa, kuma su yi kokarin gano bakin zaren warware matsalar da ake fuskanta ta hanyar diplomasiyya.(Lubabatu)