logo

HAUSA

Putin ya sanya hannu kan umarnin ’yancin kan yankuna biyu na gabashin Ukraine

2022-02-22 09:52:12 CRI

Putin ya sanya hannu kan umarnin ’yancin kan yankuna biyu na gabashin Ukraine_fororder_220222-Ahmad-Putin

A jiya Litinin shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin ya rattaba hannu kan wasu umarni biyu dake nuna amincewa da samun ’yancin kan “jamhuriyar Lugansk (LPR)" da “jamhuriyar Donetsk (DPR)" a matsayin kasashe masu cin gashin kansu.

A wani bikin da aka gudanar a fadar Kremlin, Putin ya kuma sanya hannu kan yarjejeniyar kawance, da hadin gwiwa, da cudanyar tallafawa juna tsakanin Rasha da LPR da kuma DPR, tare da shugabannin jamhuriyoyin biyu, kamar yadda fadar Kremlin ta sanar.

Rikicin tabarbarewar yanayin tsaro a kasar ta yankin Turai na faruwa ne sakamakon fadada ikon kungiyar hadin gwiwar tsaro ta NATO a gabashin kasar, lamarin da ya haddasa rashin jituwa a tsakaninta da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin.

Yayin da Moscow ta bukaci Amurka da kungiyar tsaro ta NATO, su bayar da tabbacin tsaro, kasashen yammacin duniya sun yi watsi da babbar damuwar da Rashar ke nunawa, kuma babu wata matsaya da suka canza, in ji mista Putin.

Bayan amincewa da ’yancin kan jamhuriyar LPR da DPR, Putin ya bada umarni ga rundunar sojojin Rasha da su tabbatar da zaman lafiya a kasashen biyu. (Ahmad Fagam)