logo

HAUSA

Mutane miliyan 4 sun kalli gasar Beijing Olympic ta kafar Finnish TV

2022-02-22 11:15:53 CRI

Mutane miliyan 4 sun kalli gasar Beijing Olympic ta kafar Finnish TV_fororder_220222-Ahmad-Olympics

Adadin mutanen da suka kalli gasar wasannin Olympic ta lokacin hunturu ta Beijing, a shirin kai tsaye na Yle na babbar tashar talabijin ta kasar Finland ya kai miliyan 3.9, daga cikin adadin mutanen kasar miliyan 5.5.

A sanarwar da kamfanin kula da kafar yada labaran Finnish TV ta fitar, ta ce, tsakanin ranar 4 ga watan Fabrairu zuwa 20 ga wata, shirin Yle ya watsa shirye shirye na sa’o’i 280 dake shafar wasannin Olympic a tashar TV. Nau’in gasar tsallake iyakoki a kan dusar kankara na bangaren maza, wanda aka gudanar a ranar 13 ga watan Fabrairu, shi ne ya fi samun adadin ’yan kallo mafi yawa, wanda ya kai 1,573,000.

Yle Areena, kamfanin kula da watsa shirye-shirye na kasar, ya samu adadi mafi girma a tarihi na masu kallon wasannin. Shirin intanet na Yle ya samu masu bibiyar bidiyo kimanin miliyan 38, kuma an yada shirin sau miliyan 6.1 a cikin ’yan sa’o’i, ta hanyoyin sauti da hotuna. Alkaluman sun kafa muhimmin tarihi a wasannin motsa jiki na lokacin hunturu. Idan aka yi la’akari da yanayin wasannin lokacin zafi, an samu kafa tarihi mai yawa ne ta hanyar yada shirin wasannin ta intanet, a cewar daraktan shirin wasanni na Yle, Joose Palonen.

Ya ce, gasar wasannin Olympic ta lokacin sanyi ta Beijing ta tabbatar a fili cewa, mutanen Finland suna sha’awar wasannin lokacin sanyi. (Ahmad)