logo

HAUSA

Kasar Sin ta yi kira ga bangarori daban-daban su sassauta halin da ake ciki a Ukraine ta hanyar yin shawarwari

2022-02-22 19:25:19 CRI

Kasar Sin ta yi kira ga bangarori daban-daban su sassauta halin da ake ciki a Ukraine ta hanyar yin shawarwari_fororder_11

Game da halin da ake ciki yanzu a kasar Ukraine, mai magan da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya yi jawabi a wajen taron manema labarai da aka shirya yau talata, inda ya ce, kasar Sin na sake kira ga bangarori masu ruwa da tsaki, su nuna hakuri, don sassauta halin da ake ciki da daidaita sabani ta hanyar yin shawarwari.

Da safiyar yau talata, memban majalisar gudanawar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar, Wang Yi ya zanta da takwaransa na Amurka Antony Blinken ta waya, inda suka yi musanyar ra’ayi kan batutuwan da suka shafi Ukraine da makamashin nukiliya a zirin Koriya. Wang Wenbin ya ce, kasar Sin na maida hankali sosai kan halin dake sauyawa a Ukraine. Kuma matsayin da kasar Sin ke tsayawa a kai dangane da batun kasar Ukraine bai sauya ba, wato ya kamata a mutunta kulawar duk wata kasa, kana, ya dace a kiyaye ka’idoji da manufofin kundin tsarin mulkin MDD. Tabarbarewar halin da ake ciki a Ukraine na da alaka sosai da jinkirin aiwatar da yarjejeniyar Minsk. Kasar Sin za ta ci gaba da tuntubar bangarori daban-daban bisa gaskiya da adalci. (Murtala Zhang)