logo

HAUSA

Biden zai gabatar da umarnin shugaban kasa bayan da Rasha ta amince da ’yancin kan yankunan Ukraine

2022-02-22 11:26:28 CRI

Biden zai gabatar da umarnin shugaban kasa bayan da Rasha ta amince da ’yancin kan yankunan Ukraine_fororder_220222-Ahmad-Biden

Sakatariyar yada labaran fadar shugaban kasar Amurka ta White House, Jen Psaki, ta sanar a jiya Litinin cewa, nan gaba kadan shugaban kasar Amurka, Joe Biden, zai sanya hannu kan umarnin shugaban kasa domin haramtawa Amurkawa kulla duk wata huldar cinikayya da yankuna biyu na kasar Ukrain, wadanda Rasha ta amince da samun ’yancin kansu a matsayin kasashe.

Sakatariyar yada labaran ta ce, dokar shugaban kasar daban ce da takunkuman tattalin arziki da Amurka ke shirin kakabawa Rasha, muddin ta mamaye Ukraine. Ta ce, “muna ci gaba da tuntubar kawaye da abokan huldarmu, ciki har da Ukraine, game da matakai na gaba, da kuma batun rikicin da Rasha ke haifarwa a kan iyakar Ukraine." (Ahmad Fagam)