logo

HAUSA

Xi Jinping ya aike da sakon dubiya ga sarauniyar Birtaniya Elizabeth ta II

2022-02-22 20:03:15 CRI

Xi Jinping ya aike da sakon dubiya ga sarauniyar Birtaniya Elizabeth ta II_fororder_7d9e54eff882f7b50fd00f1348bb46ceu5

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da sakon dubiya ga sarauniyar Birtaniya Elizabeth II, sakamakon kamuwa da ta yi da cutar COVID-19, inda ya yi mata fatan samun waraka cikin sauri.

Cikin sakon, Xi ya ce yana maida matukar muhimmanci ga ci gaban alakar Sin da Birtaniya, kuma Sin a shirye take ta yi aiki tare da Birtaniya, wajen gudanar da bikin cikar sassan biyu shekaru 50 da kulla huldar diflomasiyyar su a mataki na jakadanci, wanda hakan zai ingiza sabon ci gaba a alakar kasashen biyu. (Saminu)