logo

HAUSA

An kafa tawagar ‘yan wasan Olympics na lokacin hunturu na bana ajin nakasassu a Beijing

2022-02-21 19:59:29 CRI

An kafa tawagar ‘yan wasan Olympics na lokacin hunturu na bana ajin nakasassu a Beijing_fororder_d1160924ab18972b6841e2fc847590809f510acb

Za’a gudanar da gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu na bana ajin mutanen dake da bukata ta musamman a Beijing, tun daga ranar 4 zuwa 13 ga watan Maris, inda a yau ranar Litinin, aka kafa tawagar ‘yan wasannin kasar Sin. Wannan shi ne karo na shida da kasar Sin ta tura ‘yan wasanta don halartar irin wannan gasa.

Tawagar ta kunshi mutane 217 gaba daya, ciki har da ‘yan wasa 96, dake da maza 68 da mata 28, wadanda za su fafata adadin wasanni 73, a manyan nau’ikan wasannni shida.

Tawagar ‘yan wasan kasar Sin ta bana, tawaga ce mafi girma dake kunshe da ‘yan wasa mafi yawa, tun bayan da kasar ta fara halartar gasar wasannin Olympics na lokacin hunturu ajin mutanen dake da bukata ta musamman wato Paralympics. (Murtala Zhang)