logo

HAUSA

Wang Wenbin: Gasar Olympics ta Beijing nasara ce ga Sin da ‘yan Adam baki daya

2022-02-21 21:14:41 CRI

Wang Wenbin: Gasar Olympics ta Beijing nasara ce ga Sin da ‘yan Adam baki daya_fororder_VCG31N1371720278

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya ce  Gasar Olympics ta hunturu ta birnin Beijing, ta kasance nasara ga Sin da ma ‘yan Adam baki daya.

Wang ya kara da cewa, baya ga farfado da burika da kwarin gwiwa ga al’ummar duniya da annobar Covid-19 ke addabarsu, gasar ta kuma haifar da karsashi na zaman lafiya, da hadin kai a duniya.

Jami’in ya ce ‘yan wasa daga sassan kasa da kasa sun martaba, tare da goyawa juna baya, sun kuma yiwa juna fatan alheri, da kwantar da hankulan juna, ko da kuwa ba su yi nasara ba. Wadannan hotuna da aka gani na ‘yan wasan cike da annashuwa, sun nunawa duniya karfin hadin gwiwa ya zarce na masu fatan rarraba kan al’umma. (Saminu)