logo

HAUSA

Yan sandan Najeriya sun kama sama da dalar Amurka miliyan 4 na jabu

2022-02-21 10:29:53 CRI

Yan sandan Najeriya sun kama sama da dalar Amurka miliyan 4 na jabu_fororder_0221-kudi-Ahmad2

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya NDLEA, ta sanar cewa, jami’an ’yan sandan kasar masu yaki da miyagun kwayoyi sun yi nasarar gano kudaden jabu inda suka kwace kudaden jabun da darajarsu ta kai ta dala miliyan 4.7.

An kama mutum guda da ake zargi da hannu kan samar da kudaden jabun, wanda aka kama a ranar Juma’a a Abuja, babban birnin kasar, kamar yadda kakakin hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi ya bayyana.

Ya ce sun yi nasarar kwace kudaden jabun ne bayan samun bayanan sirri da hukumar ta yi tun daga inda aka dauko kudaden. Ya kara da cewa, tun da safiyar Juma’a ne jami’an hukumar suka yi nasarar kwace kudaden da aka aika daga Legas, cibiyar kasuwancin Najeriya zuwa birnin tarayyar kasar Abuja.

Babafemi ya ce, hukumar NDLEA ta bayar da umarnin mika kudaden da wadanda ake zargi ga sashen yaki da haramtattun kwayoyi na hukumar don zurfafa bincike. (Ahmad)