logo

HAUSA

Macron da Putin sun tattauna ta wayar tarho kan Ukraine tare da jaddada bukatar amfani da matakan diflomasiyya

2022-02-21 10:03:47 CRI

Macron da Putin sun tattauna ta wayar tarho kan Ukraine tare da jaddada bukatar amfani da matakan diflomasiyya_fororder_0221-Rasha-Faransa-Ahmad

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron, da takwaransa na Rasha Vladimir Putin, sun yi alkawarin kaucewa ruruta wuta, da rage barazana, da kuma tabbatar da dorewar zaman lafiya a gabashin Ukraine, yayin da shugabannin biyu suka tattauna ta wayar tarho a ranar Lahadi, fadar shugaban kasar Faransa ne ta bayyana hakan a sanarwar da ta baiwa manema labarai.

A cewar sanarwar fadar Elysee, Macron da Putin sun amince su sake yin aiki karkashin daftarin yarjejeniyar Normandy bisa ga tsarin cudanya da juna da kuma bukatun da Ukraine ta gabatar a kwanakin baya bayan nan, da kuma samun damar gudanar da taron tattaunawa na tuntubar juna tsakanin bangarori uku wanda za a gudanar nan da wasu sa’o’i masu zuwa da nufin lalibo bakin zaren tabbatar da tsakaita bude wuta daga dukkan bangarorin masu ruwa da tsaki kan rikicin.

Shugabannin sun kuma amince da bukatar bada fifiko kan amfani da matakan diflomasiyya don warware rikicin dake faruwa a halin yanzu, tare da yin dukkan abin da ya dace don cimma nasarar kawo kashen wutar rikicin. Bugu da kari, sanarwar ta ce, ministar hulda da Turai da harkokin waje na kasar Faransa, Jean-Yves Le Drian, zai gana da takwaransa na kasar Rasha, Sergei Lavrov, nan da wasu kwanaki masu zuwa, sannan za a gudanar da jerin tuntubar juna a tsakanin bangarorin a birnin Paris. (Ahmad)