logo

HAUSA

Sin tana maraba da ziyarar jami’ar kare hakkin dan adam ta MDD a Xinjiang

2022-02-20 17:04:55 CRI

Sin tana maraba da ziyarar jami’ar kare hakkin dan adam ta MDD a Xinjiang_fororder_320

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya ce, kasar Sin tana maraba da zuwan babbar jami’ar kare hakkin dan adam ta MDD Michelle Bachelet, wacce zata ziyarci kasar, ciki har da yankin Xinjiang.

Wang, wanda ya halarci taron kolin al’amurran tsaro na Munich karo na 58 ta kafar bidiyo, ya yi furucin ne a yayin da ya mayar da martani dangane da batun dake shafar yankin Xinjiang mai cin gashin kansa na Uygur na kasar Sin.

Ya bayyana cewa, Xinjiang wani yankin ne dake kan iyakar wurare masu fuskantar barazanar mayakan ‘yan ta’adda da masu tsattsauran ra’ayi, Wang yace, domin tabbatar da tsaron lafiyar al’umma, gwamnatin yankin Xinjiang, tana daukar matakan sauya tunanin masu tsattsauran ra’ayin ta hanyar ilmantarwa, wanda yayi daidai da manufofin kasashen duniya da suka hada da Birtaniya, da Faransa, da kuma al’adar kasa da kasa.

Wadannan matakai sun yi matukar tasiri wajen kawar da akidun masu tsattsauran ra’ayi, kuma sun samu gagarumin goyon bayan al’ummar yankin Xinjiang, in ji mista Wang, ya kara da cewa, a cikin shekaru biyar da suka gabata, ba a samu hare haren ta’addanci ba a yankin.

Ya ce, kasar Sin tana maraba da baki daga kasashen waje su ziyarci yankin Xinjiang domin sanin hakikanin gaskiya kan lamarin. Ya kara da cewa, kafin barkewar annobar COVID-19, yankin Xinjiang ya karbi bakuncin sama da jami’an gwamnatoci dubu 2, da masu ruwa da tsaki a harkokin addinai, da ma ‘yan jaridu daga kasashe sama da 100 da kungiyoyin kasa da kasa.(Ahmad)