logo

HAUSA

Gobara ta kashe mutane 3 a sansanin tsugunar da mutane a arewa maso gabashin Najeriya

2022-02-20 16:38:38 CRI

A kwalla mutane uku ne suka mutu a hadarin gobara wadda ta tashi a wani sansanin tsugunar da mutane IDPs, a jahar Borno, dake shiyyar arewa maso gabashin Najeriya.

Yabawa Kolo, babban daraktan hukumar bada agajin gaggawa na jahar Borno, wanda ya kai ziyarar tantance irin hasarar da aka yi sansanin Muna El-Badawy dake Maiduguri, babban birnin jahar, ya bayyana cewa, gobarar ta lalata wuraren zama kimanin 3,000, yayin da gomman magidanta suka rasa muhallansu.

A cewar jami’in, gobarar, wacce ta fara tashi a cikin wani tanti, daga bisani ta fantsama zuwa sauran wuraren kwana, sakamakon rashin kai daukin gaggawa daga jami’an kashe gobara zuwa sansanin a lokacin da lamarin ya faru.

Kolo yace, yawaitar tashin gobara a irin sansanin da kuma unguwannin dake daura da sansanin ya zama tamkar ruwan dare.

Hukumar bada agajin gaggawar tana cigaba da tantancewa domin tabbatar da girman hasarar da aka tafka, ya kara da cewa, mutanen da lamarin ya shafa suna cikin yanayin tsananin bukatar taimakon abinci, da wurin zama da sauran kayayyakin bukatun yau da kullum.(Ahmad)