logo

HAUSA

Jami’in BOCOG: Nasarar gasar Olympic ta Beijing 2022 sakamakon hadin gwiwa ne na dukkan bangarori

2022-02-20 21:22:36 CRI

Jami’in BOCOG: Nasarar gasar Olympic ta Beijing 2022 sakamakon hadin gwiwa ne na dukkan bangarori_fororder_7acb0a46f21fbe0926499032c3fae63a8744ad21

Yayin da gasar wasannin Olympic ta lokacin sanyi ta Beijing 2022 ta shiga ranar karshe, kwamitin shirya gasar wato (BOCOG), ya bayyana godiyarsa, kana yayi tsokaci game da dalilan da suka sanya gasar ta samu cikakkiyar nasara, a yayin taron manema labarai da aka gudanar a yau Lahadi.

“Gasar wasannin Olympic ta Beijing ta lokacin sanyi, ta gudana cikin nasara, kuma ta samu kyakkyawan yabo daga al’ummun kasa da kasa," a cewar mataimakin shugaban kwamitin shirya gasar ta wasannin Olympic ta lokacin hunturu ta Beijing, Zhang Jiandong, ya kara da cewa, “kasar Sin ta cika alkawarin da ta daukawa al’ummar kasa da kasa," ta hanyar karbar bakuncin gasar wasannin Olympic ta lokacin sanyi kamar yadda aka tsara duk da yanayin da ake fama da shi na annobar COVID-19.

A cewar Zhang, muhimman matakan kandagarkin yaduwar cutar da aka dauka sun kasance a matsayin babban ginshikin da ya tabbatar da samun nasarar.

Zhang ya ce, gagarumin goyon bayan da al’ummar kasa da kasa suka bayar shi ma ya taka muhimmiyar rawa wajen tsara harkokin gasar.

Ya kara da cewa, hadin gwiwar dukkan al’ummar da abin ya shafa ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen samun nasarar shirya gasar wasannin.(Ahmad)