logo

HAUSA

CPC da majalisar gudanarwar Sin sun taya tawagar ‘yan wasan kasar Sin murnar nasarorin da suka samu a gasar Olympics ta lokacin sanyi

2022-02-20 17:22:27 CRI

CPC da majalisar gudanarwar Sin sun taya tawagar ‘yan wasan kasar Sin murnar nasarorin da suka samu a gasar Olympics ta lokacin sanyi_fororder_9f6a99d536f24505a8c765c33079634d

Kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin (CPC), da majalisar gudanarwar kasar, sun aike da sakon taya murna ga tawagar ‘yan wasan kasar Sin bisa gagaruman nasarorin da suka cimma a gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu ta Beijing 2022.

Tawagar ‘yan wasan Sinawa tayi nasarar lashe lambobin zinare tara, da na azurfa hudu, da kuma na tagulla biyu, wanda ya kasance sakamako mafi kyau da kasar ta samu a tarihin gasar wasannin Olympic ta lokacin hunturu da kasar Sin ta halarta.

An yabawa tawagar bisa yadda suka daukaka kasar Sin da al’ummar Sinawa a idon duniya, kana sun bayar da muhimmiyar gudunmawa ga samun nasarar karbar bakuncin gasar ta wasannin Olympic ta lokacin hunturu ta Beijing.(Ahmad)