logo

HAUSA

Shugaban kwamitin shirya wasannin Olympics na kasa da kasa ya sake hira da ‘yan jaridun CMG

2022-02-20 20:17:17 CRI

Shugaban kwamitin shirya wasannin Olympics na kasa da kasa ya sake hira da ‘yan jaridun CMG_fororder_微信图片_20220220191504

Kafin rufe gasar wasannin Olympics na lokacin hunturu na bana a Beijing, shugaban kwamitin shirya gasar wasannin Olympics na kasa da kasa wato IOC, Thomas Bach ya sake zantawa da ‘yan jaridun CMG, babban rukunin gidan rediyo da talabijin na kasar Sin.

Bach ya bayyana cewa, ‘yan wasannin kasa da kasa sun shaidawa duniya kyawawan halayensu, da bayyana ma’anar zumunci da samun fahimtar juna da zaman lafiya. Alal misali, ‘yan wasannin Ukraine da Rasha sun rungumi juna, kana, ‘yan wasan kasar Sin sun goyi bayan ‘yan wasan Amurka, har sun ba su tambarin Olympics kyauta don nuna son karbar baki. Akwai irin wadannan misali da dama, wadanda suka nuna cewa wasan Olympics zasu iya yin galaba kan fito-na-fito na rikicin siyasar duniya.

Mista Bach ya kara da cewa, kafar CMG ta samu gagarumar nasara wajen gabatar da shirye-shirye gami da watsa rahotanni game da gasar ta bana, kuma yana da yakinin cewa hadin-gwiwar IOC da CMG za ta dada inganta. (Murtala Zhang)