logo

HAUSA

Wang Yi ya halarci taron tsaro na Munich ta kafar bidiyo

2022-02-19 20:59:00 CRI

Wang Yi ya halarci taron tsaro na Munich ta kafar bidiyo_fororder_王毅

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya halarci taron tsaro na Munich, karo na 58, yau Asabar ta kafar bidiyo.

Da yake jawabi, Wang Yi ya ce dukkan kasashe na bukatar sauke nauyin dake wuyansu tare da kokarin neman zaman lafiya yayin da tankiya game da Ukraine ke kara kamari. (Fa’iza Mustapha)