logo

HAUSA

Kasashen Afirka 6 za su samu fasahar samar da allurar rigakafin COVID-19

2022-02-19 16:06:50 CRI

Kasashen Afirka 6 za su samu fasahar samar da allurar rigakafin COVID-19_fororder_疫苗-3

Babban sakataren hukumar lafiya ta duniya Tedros Ghebreyesus ya sanar a jiya cewa, kasashen Afirka shida da suka hada da Masar da Kenya da Najeriya da Senegal da Afirka ta kudu da kuma Tunisiya, za su samu fasahar samar da allurar rigakafin cutar COVID-19 daga hukumar, inda za su samar da allurar rigakafin cutar irin na mRNA.

Hukumar lafiya ta duniya ta zabi wadannan kasashe shida, a matsayin wadanda za su samu fasahar samar da allurar rigakafin mRNA a karo na farko a fadin duniya, domin taimakawa kasashen Afirka yayin da suke kokarin kandagarkin annobar COVID-19 da sauran cututtuka.

A halin yanzu, kaso 1 bisa dari kadai, na daukacin alluran rigakafin da ake yi wa al’ummun da yawansu ya kai kusan biliyan 1.3 aka samar a nahiyar Afrika.

Hukumar lafiya ta duniya ta kafa cibiyar mika fasahar samar da allurar rigakafin mRNA ta kasa da kasa a kasar Afirka ta kudu a bara, domin nuna goyon bayanta ga kamfanonin samar da allurar rigakafi na kasashen dake fama da talauci, wajen samar da rigakafi da kansu. (Jamila)