logo

HAUSA

Jakadan kasar Sin: Sin na ingiza tattaunawa kan batun kwance damarar soji

2022-02-19 16:31:45 CRI

Jakadan kasar Sin: Sin na ingiza tattaunawa kan batun kwance damarar soji_fororder_li song

Shugaban karba karba na farko na shekarar 2022 na taron tattauna batun kwance damarar soji na birnin Geneva, kuma jakadan kasar Sin kan wannan batu, Li Song ya kira cikakken taro yayin da ya yi nasarar kammala wa’adin shugabaci na kasar Sin a jiya Juma’a. Bayan taron, Li Song, ya tattauna da kafofin watsa labarai na birnin Geneva, inda ya bayyana cewa, taron ya kasance dandali daya tilo dake tattauna batun kwance damara tsakanin bangarori daban daban, inda kasashe mambobi 65 ke karbar shugabanci daya bayan daya. Ya ce kasar Sin ta sake zama shugaba ne bayan shekaru 11 da suka gabata, kuma a cikin wadannan shekaru 11, huldar kasa da kasa da yanayin tsaronsu sun fuskanci manyan sauye-sauye, haka kuma kasashen duniya sun fuskanci kalubalen da suka hada da tsoffi da sabbabi. Ya ce a karkashin irin wannan hali, kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa wajen ingiza zaman lafiya a fadin duniya, kana tasirinta a bangaren kwance damarar soji ya kara karfafuwa, a don haka kasashen duniya suke sa ran cewa, za ta ci gaba da ba da gudummuwa ga kwance damarar soji tsakanin bangarori daban daban.

Li Sing ya jaddada cewa, nan gaba kasar Sin za ta ci gaba da nacewa kan manufar samun ci gaba cikin lumana.(Jamila)