logo

HAUSA

Kasar Sin ta yi kira da a kyautata tafiyar da harkokin tattalin arziki a duniya

2022-02-19 16:46:38 CMG

Kasar Sin ta yi kira da a kyautata tafiyar da harkokin tattalin arziki a duniya_fororder_0219-kudi-G20-Fa'iza

Ma'aikatar kudi ta kasar Sin, ta yi kira ga kasashen duniya su karfafa hadin gwiwa wajen tafiyar da dabarun da suka shafi tattalin arziki, a matsayin wata hanya ta samun ci gaba na bai daya.

Ministan kudi na kasar Sin, Liu Kun ne ya bayyana haka, yayin wani taron ministocin kudi da gwamnonin manyan bankunan kasashen G20 da ya gudana ta kafar bidiyo.

A cewar Liu Kun, cikin kasashen kungiyar G20, kasar Sin ta kasance babbar mai bayar da gudunmuwa ga shirin saukaka basussuka ga kasashe masu fama da talauci.

Ya ce Kasar Sin tana kira ga dukkan masu ruwa da tsaki, su aiwatar da matsaya da G20 ta cimma, su girmama cikakken 'yancin kasashen da ake bi bashi, su kuma inganta nasarar wannan batu a aikace.

Ya ce ya kamata masu bayar da bashi ga bangarori daban-daban kamar Bankin Duniya, su dauki matakan saukaka basussuka bisa hanyoyi masu karfi, da taimakawa kasashe masu karancin kudin shiga. (Fa’iza Mustapha)

Fa'iza