logo

HAUSA

Kafofin watsa labaran Amurka: Masu zuba jari na kasa da kasa suna kara zuba jari ga kasuwar hada-hadar kudin Sin

2022-02-19 15:42:44 CRI

Kafofin watsa labaran Amurka: Masu zuba jari na kasa da kasa suna kara zuba jari ga kasuwar hada-hadar kudin Sin_fororder_jari

Tashar yanar gizo dake ba da labaran sayayya da kasuwanci ta Amurka ta wallafa wani rahoto a ranar 17 ga wata dake cewa, duk da cewa, masu zuba jari dake cikin gidan kasar Sin ba su nuna kuzari sosai ga kasuwar hada-hadar kudin kasar ba, masu zuba jari na kasa da kasa na kara zuba jarinsu ga kasuwar hada-hadar kudin kasar Sin. Alkaluma sun nuna cewa, a watan Janairun bana, adadin kudin da aka zuba kan kasuwar hada-hadar kudin kasar Sin ya kai dalar Amurka biliyan 16.6, wannan kuma shi ne karo na hudu da adadin ya zarta dala biliyan 10 a cikin wata guda, tun bayan barkewar annobar cutar COVID-19.

An lura cewa, a cikin ‘yan watannin da suka gabata, kamfanonin zuba jari dake fadin duniya suna kara nuna kuzari kan kasuwar hada-hadar kudin kasar Sin, inda kasar ta kasance zabi mai inganci a bangaren zuba jari a bana. (Jamila)