logo

HAUSA

Shugaban IOC Ya Yaba Da Fasahar CMG

2022-02-18 14:22:58 CRI

Shugaban IOC Ya Yaba Da Fasahar CMG_fororder_ioc

Ranar 18 ga wata, shugaban kwamitin wasan Olympic na kasa da kasa wato IOC ya shirya taron manema labaru, inda shugaban kwamitin Thomas Bach ya ce, yayin da ake gudanar da gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing, an gwada fasahohi iri daban daban, musamman ma mabambantan fasahohin zamani mallakar babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin na CMG, wadanda suka ba shi mamaki sosai. Ya yi imanin cewa, fasahohin kasar Sin za su kara ba da gudummowa kan wasannin Olympics a nan gaba.

Shugaban IOC ya kara da cewa, an samu nasara sosai a gasar ta Beijing, inda ‘yan wasa suka ji dadi sosai, sun kuma gamsu sosai kan filayen wasa, kauyen Olympic, hidimomi masu ruwa da tsaki da ma yadda ake yaki da annobar COVID-19. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan