logo

HAUSA

Sin: Ya kamata a aiwatar da yarjejeniyar Minsk idan ana son warware matsalar Ukraine

2022-02-18 12:33:08 CRI

Sin: Ya kamata a aiwatar da yarjejeniyar Minsk idan ana son warware matsalar Ukraine_fororder_2f738bd4b31c87018c5dc3b89c1f79260608ff6b

Jiya 17 ga wata, kwamitin sulhun MDD ya kira taro kan batun Ukraine, don tattaunawa kan yadda ake aiwatar da yarjejeniyar Minsk. Inda Zhang Jun, zaunannen wakilin kasar Sin a MDD ya bayyana ra’ayin kasar Sin kan halin da Ukraine ke ciki, tare da jaddada cewa, ya kamata a aiwatar da yarjejeniyar idan ana son warware matsalar kasar.

Zhang Jun ya bayyana cewa, a halin yanzu, ya kamata bangarori daban daban su kai zuciya nesa, tare da bin hanyar warware batun Ukraine a siyasance, a kaucewa duk wani abin da zai tsananta halin da ake ciki ko ruruta wuta kan batun. Ya dace bangarorin da lamarin ya shafa su warware rikicin dake tsakaninsu ta hanya mafi dacewa bisa tushen kulawa da muradun juna da gimamawa juna.

Ban da wannan kuma, Zhang Jun ya ce, fadada girman kungiyar tsaro ta NATO wani batu ne da ya kamata a warware idan ana son daidaita batun Ukraine. Bayan an kawo kashen yakin cacar baki, kungiyar NATO na ci gaba da kokarin fadada girmanta, lamarin da ya saba da manufar kiyaye tsaron kowa da kowa. Bai kamata a lahanta tsaron sauran kasashe don wai kiyaye tsaron wata kasa ba, haka kuma bai kamata a ci gaba da fadada girman wata kungiyar soja don wai tabbatar da tsaron wani yanki ba. (Kande Gao)