logo

HAUSA

Gu ta lashe gasar al-kafura a tuddan kankara ta mata inda ta samu lambar zinarenta na biyu a gasar Olympic ta Beijing 2022

2022-02-18 16:09:06 CRI

Gu ta lashe gasar al-kafura a tuddan kankara ta mata inda ta samu lambar zinarenta na biyu a gasar Olympic ta Beijing 2022_fororder_220218-Ahmad5-谷爱凌

Kwararriyar ’yar wasan zamiyar kankara ta kasar Sin Gu Ailing, ta cimma nasara a rukunin gasar al-kafura a tuddan kankara ta halfpipe a gasar wasannin motsa jiki ta lokacin hunturu ta Beijing 2022 a yau Juma’a, wanda kuma shi ne lambar zinare na biyu da ’yar wasan ta ciyowa kasar Sin mai karbar bakuncin gasar.

A zagaye na uku na karshen gasar, ’yar wasan zamiyar kasar Kanada  Cassie Sharpe, ta samu lambar azurfa.

Sannan Rachael Darker, ta lashe lambar tagulla, wacce ita ma ’yar kasar Kanada ce. (Ahmad)