logo

HAUSA

Kasar Sin Ta Cimma Manufar Shigar Da Mutane Miliyan 300 Cikin Wasannin Kankara

2022-02-18 11:32:34 CRI

Kasar Sin Ta Cimma Manufar Shigar Da Mutane Miliyan 300 Cikin Wasannin Kankara_fororder_kankara

Yayin da kasar Sin ke neman bakuncin shirya gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi ta shekarar 2022, ta yi wa kasashen duniya alkawarin shigar da mutane miliyan 300 cikin wasannin kankara. Bayan da ta samu nasarar karbar bakuncin shirya gasar a shekarar 2015 har zuwa yanzu, wasannin kankara sun zama wata hanyar jin dadin zama a tsakanin al’ummar kasar Sin.

Adadin kididdiga ya nuna cewa, tun bayan da kasar Sin ta samu damar karbar bakuncin shirya gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi ta shekarar 2022 ya zuwa watan Oktoban shekarar 2021, yawan mutanen da suka shiga wasannin kankara ya kai miliyan 346 a duk kasar baki daya. Sin ta cika alkawarinta na shigar da mutane miliyan 300 cikin wasannin kankara, wanda shi ne sakamako mafi girma da aka samu sakamakon shirya gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing.

Aikin yawon shakatawa a wurare masu kankara ya samu saurin bunkasuwa a kasar Sin. Alkaluma sun nuna cewa, yawan zirga-zirgar mutanen da suka shakata a wurare masu kankara ya kai miliyan 230 a kasar Sin, kana yawan kudin shigar da aka samu a fannin ya wuce kudin Sin RMB yuan biliyan 390. An kiyasta cewa, yawan zirga-zirgar mutanen da za su shakata a wurare masu kankara zai iya kaiwa miliyan 305 daga shekarar 2021 zuwa 2022 a kasar Sin. Wasannin kankara na kara taka muhimmiyar rawa wajen farfado da yankunan karkara, sauya salon raya wurare da tabbatar da samun bunkasuwar tattalin arziki mai dorewa da ci gaban kasa mai inganci. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan