logo

HAUSA

Yawan jarin waje da aka zuba a kasar Sin ya karu da kaso 11.6% a Janairu

2022-02-17 11:06:42 CRI

Yawan jarin waje da aka zuba a kasar Sin ya karu da kaso 11.6% a Janairu_fororder_faf2b2119313b07eee8ccb09bd23722a96dd8cf8

Kididdigar da ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta fitar ta yi nuni da cewa, a watan Janairun shekarar 2022, yawan jarin waje da aka zuba a kasar Sin ya kai kudin Sin yuan biliyan 102.28 kwatankwacin dalar Amurka biliyan 15.84, adadin da ya karu da kashi 11.6% bisa na makamancin lokacin bara. Idan kuma an yi nazari, za a gane cewa, jarin da kasashen da suka amsa shawarar “ziri daya da hanya daya” da ma kasashen kungiyar ASEAN suka zuba ya karu da kimanin 30%.

A game da wannan, Mr Zhang Jianping, darektan cibiyar nazarin hadin gwiwar tattalin arzikin shiyya-shiyya karkashin kwalejin nazari na ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin ya yi nuni da cewa, jarin waje da ake zubawa a kasar Sin na ci gaba da karuwa yadda ya kamata bayan jarin da aka zuba a kasar ya zarce kudin Sin yuan triliyan guda a bara. Yana mai cewa,“Kaso 11% ba karamar karuwa ba ce, wanda ya shaida cewa, a yayin kokarin neman farfadowar tattalin arzikin duniya, duk da matsalolin da ake fuskanta, kasar Sin na kara janyo jari daga kasashen ketare sakamakon yadda tattalin arzikin kasar ke gudana yadda ya kamata da ma dokar zuba jari ta baki ’yan kasuwa da yankin gwajin ciniki maras shinge da aka kafa a kasar da ma yarjejeniyar ciniki mai ’yanci da aka cimma da kyautatuwar yanayin kasuwanci na kasar da girman kasuwarta da sauransu.”  (Lubabatu)