logo

HAUSA

Sufurin jiragen saman dakon kaya na Sin ya kusa kaiwa gabanin barkewar annoba a watan Janairu

2022-02-17 11:21:11 CRI

Sufurin jiragen saman dakon kaya na Sin ya kusa kaiwa gabanin barkewar annoba a watan Janairu_fororder_220217-A04-China-air-0217

Hukumomin kasar Sin sun bayyana cewa, a watan Janairu, an samu farfadowar harkokin sufurin manyan jiragen saman dakon kayayyaki na kasar wanda ya kusan kaiwa matsayin na gabanin lokacin barkewar annoba.

Adadin jiragen dakon kaya da sakonnin da aka yi jigilarsu ta jiragen sama ya kai kimanin ton 654,000 a watan Janairu, ko kuma kashi 97.3 bisa 100 na adadin da aka samu a makamancin lokacin shekarar 2019, kamar yadda hukumar kula da harkokin sufurin jiragen saman kasar Sin CAAC ta bayyanawa taron ’yan jaridu.

A cewar hukumar, matsayin farfadowar da aka samu ya karu da kashi 6.6 bisa 100 daga watan Disambar 2021.

A watan Janairu, adadin ya karu da kashi 1.1 bisa 100 daga watan da ya gabata, amma adadin ya ragu da kashi 2.3 bisa 100 daga makamancin lokacin shekarar da ta gabata.

Alkaluman hukumar CAAC sun nuna cewa, hukumar kula da kamfanonin sufurin jiragen saman kasar ta gudanar da aikin jigilar fasinjoji miliyan  29.51 a watan jiya, adadin da ya ragu da kashi 2.2 a bisa na makamancin lokacin shekarar bara. (Ahmad)