logo

HAUSA

IOC ya nuna babban yabo kan matakan dakile COVID-19 a gasar Beijing 2022

2022-02-17 10:40:29 CRI

IOC ya nuna babban yabo kan matakan dakile COVID-19 a gasar Beijing 2022_fororder_220217-A01-IOC gives high praise for COVID

Kwamitin shirya gasar wasannin motsa jiki na Beijing 2022, BOCOG, ya sanar da cewa, an samu rahoton kamuwa da cutar COVID-19 guda biyu wanda ke da alaka da gasar Olympic ta lokacin sanyi ta Beijing 2022 a ranar Talata, daya an samu ne a sakamakon gwajin da aka yi bayan isowa, yayin da na biyu an samu ne bayan kammala dukkan gwaje-gwajen.

Kwamitin shirya gasar wasannin Olympic ta kasa da kasa (IOC), ya yi matukar nuna yabo game da matakan kandagarkin cutar da ake dauka a gasannin. Kakakin kwamitin IOC, Mark Adams ya ce, "ina tunanin a wasu lokutan har muna mantawa da cewa muna tsakiyar fama da annoba. Kuma muna karbar bakuncin gasa ko dai mafi sarkakiya ko kuma gasar wasanni mafi samun nasara a duniya." Ya kara da cewa, "hankalinmu bai gama kwantawa ba. Saboda har yanzu ba a kammala gasar ba." "A yanzu muna kokarin ganin kowa ya bar wannan wuri lami lafiya. Wannan shi ma babban kalubale ne bisa shirin da muka tsara. Amma da farko dole ne na jinjinawa abokanmu Sinawa da abokan aikinmu. Wannan gagarumin aiki ne."

Huang Chun, mataimakin babban daraktan ofishin yaki da annobar na kwamitin gasar wasannin ta BOCOG, ya danganta ingancin matakan dakile annobar bisa ga amfani da hanyoyin kimiyya da bin hakikanin matakan yaki da annobar dake kunshe cikin littafin ka’idojojin yaki da annobar, wanda ake sabuntawa daga lokaci zuwa lokaci da kuma cikakken hadin kai da jami’ai ke bayarwa. (Ahmad Fagam)