logo

HAUSA

Wang Wenbin: Sin ta aiwatar da bukatar dagewa kasashe matalauta bashin da take bin su

2022-02-17 19:31:20 CRI

A yau Alhamis ne kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyanawa taron manema labarai cewa, bisa matsayar da aka cimma tsakanin kasashe mambobin kungiyar G20, Sin ta aiwatar da bukatar dagewa kasashe mafiya fama da talauci wa’adin bashin da take bin su, inda ta zamo kasa mafi bin tarin bashi, da ta samar da wannan sassauci a cikin dukkanin mambobin kungiyar ta G20.

Wang Wenbin ya kara da cewa, kamar yadda sassan hukumomin kasa da kasa masu nasaba da lamarin suka fayyace, sassan da aka fi dagewa biyan bashi mafi tsoka, sun hada da kasashe matalauta dake da tarin bashi a kan su, da bankunan samar da ci gaba na kasa da kasa, da cibiyoyin ba da lamuni masu zaman kan su, kamar bankunan cinikayya dake kasashe masu tasowa.

Jami’in ya ce alal misali, cikin jimillar basukan waje na kasashen Afirka, cibiyoyin hada hadar kudade na kasa da kasa, da bankunan ba da lamuni su ne ke da bashin kasar Sin, da ya kai kaso sama da 3/4. Don haka suna da muhimmin tasirin sauke nauyin bashin dake kan kasashen su. Kaza lika suna da babban nauyi na taimakawa ci gaban kasashen su a fannin rage yawan bashi. (Saminu)