logo

HAUSA

Faransa da Canada sun ayyana janye sojojin su daga Mali

2022-02-17 19:39:05 CRI

Faransa da Canada sun ayyana janye sojojin su daga Mali_fororder_macron

A yau Alhamis 17 ga watan Fabarairu, shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron, ya kira taron manema labarai a fadar gwamnati, inda ya bayyana cewa, kasar sa da kawayen ta na Turai da Canada, za su fara janye dakarun sojin su dake kasar Mali tun daga yau Alhamis.

Faransa ta fara taimakawa kasar Mali a fannin yaki da ayyukan ta’addanci tun daga shekarar 2013. To sai dai kuma gwamnatin Mali ta yanzu, ta bukaci dakarun sojin kasashen yamma da su fice daga kasar ba tare da bata lokaci ba, lamarin da ya tilastawa Faransa da kawayen ta, gaggauta yanke shawarar janye sojojin su daga kasar.   (Saminu)