logo

HAUSA

Liyafar bikin Yuan Xiao ta CMG ta nuna yadda al’adun Sin da fasahohin zamani suka hadu da juna

2022-02-16 13:38:54 CRI

Liyafar bikin Yuan Xiao ta CMG ta nuna yadda al’adun Sin da fasahohin zamani suka hadu da juna_fororder_hoto3

A daren ranar 15 ga wata, wato ranar 15 ga watan farko bisa kalandar gargajiyar kasar Sin, babbar kafar yada labarai ta kasar Sin wato CMG ta gabatar da liyafar bikin Yuan Xiao ta shekarar 2022. Babban taken liyafar ita ce “farin cikin bikin Yuan Xiao, da nishadantuwa da al’adun Sinawa”, inda aka nuna shirye-shiryen raye-raya da wakoki da fasahar Kongfu da wasan kwaikwayon gargajiyar kasar Sin da dai sauransu.

Cikin shiri na farko mai taken “Dadin Kowa”, tare da masu kide-kide, ’yar saman jannati na kasar Sin Wang Yaping ta yi kidar waka ta “furannin Jasmine” cikin tashar sararin samaniya ta kasar Sin, inda suka bayyana fatan alheri ga al’ummomin kasar Sin.

Liyafar bikin Yuan Xiao ta CMG ta hada al’adun kasar Sin da fasahohin zamani tare, inda jama’ar kasar Sin suka nishadantu da shirye-shiryen da ta shirya sosai. (Maryam)