logo

HAUSA

Me shugaban IOC ya shaidawa jagoran CMG?

2022-02-16 20:31:02 CRI

Me shugaban IOC ya shaidawa jagoran CMG?_fororder_CMG

A jiya Talata ne shugaban kwamitin shirya gasar Olympic ta kasa da kasa IOC Thomas Bach, ya mikawa shugaban babbar kafar watsa shirye shirye ta kasar Sin CMG Shen Haixiong, kofin karramawa a nan birnin Beijing, bisa gudummawar da shi kan sa, da ma CMGn suka bayar, wajen watsa wasannin wannan muhimmiyar gasa.

Yayin da yake karbar wannan kyauta, Shen Haixiong ya ce wannan nasara ce ta daukacin masu ruwa da tsaki, kuma wannan karramawar ta IOC, ta tabbatar da kwazon CMG, da ma daukacin kafofin watsa shirye shirye na Sin, bisa kokarin su na yayata ruhin Olympic, da watsa shirye shiryen gasar ta birnin Beijing.   (Saminu)