logo

HAUSA

Dan Nigeria dake karatu a kasar Sin ya jinjinawa gasar wasannin Olympics ta Beijing

2022-02-16 11:05:28 CRI

Dan Nigeria dake karatu a kasar Sin ya jinjinawa gasar wasannin Olympics ta Beijing_fororder_0216-Nigerian student-Fa'iza

Bayyanar Rawayen Kogi a sararin samaniya, yayin bikin bude gasar Olympics ta lokacin hunturu ta Beijing, ta girgiza Ezenne Godwin Chukwuebuka, wani dan Nijeriya dake karatu a jami’ar Lanzhou dake lardin Gansu na arewa maso yammacin kasar Sin.              

A cewar Ezenne, wanda ya shafe lokaci mai tsawo yana karatu a birnin Lanzhou dake kusa da kogin, bayyanar Rawayen kogin wani kagaggen abu ne na kimiyya da aka nuna yayin bikin bude wasannin Olympics na Beijing na 2022.

Gasar ta Beijing ta samu yabo sosai daga dalibai ’yan kasashen waje kamar Ezenne, wanda ya kalli bikin bude wasannin da shirye-shirye da dama tun daga farkon watan Fabreru.

Ezenne ya kuma yi mamakin ganin wani dan wasa dake wakiltar Nijeria a gasar. Inda ya ce duk da babu dusar kankara a kasarsa, kasashe da dama sun hadu a wasannin Olympics na lokacin hunturu, saboda abota. Yana mai cewa, kasar Sin ta zama dandalin dake taimakawa kulla zumunta tsakanin kasashe da yankuna. (Fa’iza Mustapha)