logo

HAUSA

’Yan jaridu sama da dubu 10 na kokarin watsa labaran gasar Olympics ta Beijing 2022

2022-02-16 11:45:46 CRI

’Yan jaridu sama da dubu 10 na kokarin watsa labaran gasar Olympics ta Beijing 2022_fororder_hoto2

Bayan bude gasar wasannin motsa jiki ta Olympics ta lokacin hunturu ta Beijing, ’yan jaridu na kasar Sin da na ketare sun ci gaba da watsa labarai game da wasanni bisa fannoni daban daban ga jama’ar kasa da kasa. Babbar kafar yada labarai ta gwamnatin kasar Sin ta hada gwiwa da kafofin watsa labarai 21 na kasar Sin da na kasashen ketare, domin watsa labarai game da wasannin ta hanyoyi daban daban cikin lokaci, kuma bisa fannoni daban daban. Lamarin da ya sa, al’ummomin kasashen duniya ke kara mai da hankali kan gasar.

’Yan jaridu sama da dubu 10 na kokarin watsa labaran gasar Olympics ta Beijing 2022_fororder_hoto22

Haka kuma, ’yan wasannin motsa jiki na kasashen duniya suna fafatawa cikin wasanni daban daban, inda labaransu ke jan hankulan al’ummomin kasa da kasa. Bisa kididdigar da aka yi, bayan bude gasar, akwai ’yan jaridu sama da dubu 10 da suka yi rajista a cibiyar watsa labarai ta gasar Olympics ta lokacin hunturu ta Beijing. Kuma, cikin cibiyar akwai masu aikin sa kai dake taimakawa ’yan jaridu kan batutuwan da suka shafi harsuna da yin rajista da bayanin sufuri da sauransu. (Maryam)